Ƙungiyar APC ta nemi Tinubu ya waiwayi Arewa

Kungiyar APC ta APC Northwest Reclamation front ta tunatar da gwamnatin tarayya muhimmancin warware matsalolin da su ka dabaibaye yankin.
Shugaban kungiyar, Hisham Habib ne ya yi kiran bayan taron da suka gudanar a kan matsalolin Arewa.
Ya ce manyan ayyuka a Arewa su na samun koma baya, duk da yadda mutanen shiyyar sun fi na sauran yankunan kasar nan yawa.
Hisham Habib ya kara da cewa an tabbatar da yankin Arewa shi ne ya ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kuri’ar da ya yi nasara a zaben 2023, saboda haka akwai bukatar a waiwaye su kafin zaben 2027.
Kungiyar ta zauna da mambobinta daga jihohin Kano, Kaduna, Kebbi, Zamfara, Sakkwato, Jigawa da Katsina.
Ƙungiyar APC ta nemi Tinubu ya waiwayi Arewa


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading