An nada Aisha Maikudi a matsayin shugabar jami’ar Abuja

Majalisar Zartarwa ta Jami’ar Abuja (UniAbuja), karkashin jagorancin Air Vice-Marshal Saddiq Ismaila Kaita, ta amince da nadin Professor Aisha Sani Maikudi a matsayin Shugabar Jami’ar ta bakwai na dindindin.
An sanar da nadin ne a yayin taron Majalisar 77 na Musamman a ranar Talata, 31 ga Disamba, 2024.
Nadin zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2025, kuma yana da tsawon wa’adin shekaru biyar wanda ba za a iya sabunta shi ba.
Wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai da Harkokin Jami’a na Jami’ar, Habib Yakoob, ya sanya hannu a kai, ta bayyana cewa Professor Maikudi ta zama wacce tafi cancanta daga cikin mutum goma da aka duba.
Sanarwar ta kara da cewa kafin a nada ta a matsayin Shugabar Jami’ar, Professor Aisha Sani Maikudi ta rike wannan mukamin a matsayin shugaba na rikon kwarya daga ranar 5 ga Yuli, 2024.
“A wannan lokacin, ta yi aiki tukuru da Majalisar Zartarwa domin dawo da zaman lafiya a jami’ar yayin da take fuskantar kalubale.”sanarwar ta kara da cewa.
An nada Aisha Maikudi a matsayin shugabar jami’ar Abuja


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading