Atiku yayi Allah wadai da faretin sojan da aka yiwa dan shugaban kasa Seyi Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da faretin soja da aka shiryawa ɗan Shugaban Kasa, Seyi Tinubu, yana mai bayyana shi a matsayin cin fuska ga al’adun soja.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu, Atiku ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin. Ya ce abin kunya ne ga kowane reshe na rundunar sojojin Najeriya ta shirya irin wannan fareti na soja ga wanda ba shi da matsayi na soji a hukumance.
Sanarwar ta nuna takaicin tsohon mataimakin shugaban kasar game da bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda aka ga wasu samari dauke da makamai cikin tsari na soja suna bawa ɗan shugaban kasa girmamawa ta soja. Atiku ya bayyana lamarin a matsayin abin tayar da hankali, musamman ganin cewa ƙungiyar da ake kira “Nigeria Cadet Network” da ta shirya wannan fareti ba ta da matsayi a hukumance a Rundunar Sojojin Najeriya.
Ya ce amfani da sunan “Cadet,” wanda ke nufin matasa da suka samu horo na musamman a soja, ya zubar da mutuncin rundunar.
Atiku yace “Abin mamaki shi ne yadda aka bari farar hula su yi amfani da makamai a irin wannan lokaci da ya kamata a rika kula sosai da yawaitar makamai ba bisa ka’ida ba.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan:
Sahihancin ƙungiyar “Nigeria Cadet Network” da amfani da sunan “Cadet” ba bisa ka’ida ba.
Asalin da kuma halaccin makaman da mambobin ƙungiyar suka nuna.
Dacewar girmamawar sojoji da aka bai wa ɗan Shugaban Kasa daga farar hula da sukayi basaja suka nuna soji ne.
Atiku ya ce ya zama wajibi hukumomin tsaro su kare martabar Rundunar Sojojin Najeriya. Ya kuma bukaci a dauki mataki idan aka gano an karya doka ta kowace fuska, domin tabbatar da an hukunta masu laifi.
Atiku yayi Allah wadai da faretin sojan da aka yiwa dan shugaban kasa Seyi Tinubu


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading