Ba zamu lamunci karkatar da kudin al’umma ba – Majalisar dokokin Kano

Majalisar dokokin Kano ta gargadi ma’aikatan gwamnati da hukumominta da shugabannin kananan hukumomin jihar, kan su tabbata sun yi amfani da kasafin kudin shekara mai kamawa dai-dai da yadda suka gabatar mata kuma aka amince musu.
Shugaban kwamitin kasafin kudi kuma wakilin karamar hukumar Ungogo, Aminu Sa’adu Ungogo ne ya bayyana hakan bayan da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta kammala kare kasafin kudinta.
Ya ce majalisar za ta matsa kaimi ta hanyar yin amfani da kwamitocinta wajen bibiyar dukkanin ayyukan da ma’aikatu, hukumomi da kananan hukumomin su ka gabatar mata domin tabbatar da cewa ba’a karkatar da kudaden al’umma ba zuwa aljihun wasu.
Majalisar dokokin ta Kano ta sha alwashin sanya kafar wando daya da duk ma’aikata ko hukumar da aka samu da sabawa tsarukan da gwamnati ta shiryo.
Ba zamu lamunci karkatar da kudin al’umma ba – Majalisar dokokin Kano


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading