Bauchi: Shettima, Dangote da gwamnoni sun halarci bikin dan Bagudu

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima tare da wasu fitattun mutane sun hallara domin bikin daurin auren Ibrahim A. Bagudu, ɗan Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren, Atiku Bagudu, da Amina Tatari Ali, a Kaduna a ranar Juma’a.
Bikin ya gudana ne a masallacin Sultan Bello mai dimbin tarihi, inda manyan baki suka halarta, ciki har da gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris; gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum; da attajirin Afrika, Aliko Dangote.
Haka nan, hwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun; gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; Ministan Tltsaro, Muhammad Badaru Abubakar; da Ministan kuÉ—i, Wale Edun, sun kasance a wajen taron.
Daurin auren ya samu jagorancin Bmbabban limamin masallacin Sultan Bello, Dr. Muhammad Suleiman Adam, wanda ya yi addu’o’in zaman lafiya da farin cikin ma’auratan.
A cikin wa’azinsa, limamin ya jaddada muhimmancin soyayya, haɗin kai, da imani wajen gina tushen iyali mai ƙarfi.
 
Bauchi: Shettima, Dangote da gwamnoni sun halarci bikin dan Bagudu


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading