Dasa bam a hanya ba zai hana jami’an tsaro maganin yan bindiga ba – Gwamna Lawal

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa dabarar da ’yan bindiga suka dauka kwanan nan na dasa bam a hanya na son hana sojojin da hukumomin tsaro kaiwa maboyarsu.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta karkata daga nufinta na yaki da rashin tsaro ba, duk da matsalolin da wasu masu ruwa da tsaki ke haddasawa, suna kokarin kawo cikas ga kokarinsa na yaki da ‘yan ta’adda da sauran laifuka a jihar.
Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake bude yaron yankin Arewa maso Yamma na daraktocin tsaro na kihohi, wanda jukumar Tmtsaro ta DSS ta shirya a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Gwamnan, wanda Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya wakilta, ya ce sabon salo da ’yan bindiga suka dauka na dasa abubuwan fashewa a wuraren da ba su da tsaro wata dabara ce ta rashin jarunta da ke nuna suna fuskantar matsin lamba.
“Muna aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile wannan mummunan yanayi na rashin tsaro a jihar mu.”
“Sabuwar dabarar da ’yan bindiga suka dauka ta amfani da abubuwan fashewa wani yunkuri ne na hana sojoji kaiwa maboyarsu tare da kokarin razana mazauna yankunan domin su mika wuya ga barazanar su.”
Gwamnan ya kuma yi kira da a tattauna kan ayyukan kungiyar Lukurawa domin tabbatar da cewa ba su zama barazana ga tsaro ba.
“Ayyukan kungiyar Lukurawa, musamman a yankinmu, sun zama batun tattaunawa bangaren tsaro.”
“Wadannan matsaloli suna nuna bukatar duba yanayin tsaro a kai a kai, kuma ina fatan wannan taron zai ba da fifiko wajen tattauna wannan sabon yanayi.”
Dasa bam a hanya ba zai hana jami’an tsaro maganin yan bindiga ba – Gwamna Lawal


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading