Dattijan Arewa, Matasa sun nemi shugaban Nijar ta nemi afuwar Najeriya

Wasud aga cikin Dattawan Arewacin Najeriya da kungiyoyin matasa sun yi watsi da zargin da Shugaban Sojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, cewa ya haɗa kai da ƙasar Faransa don tada hankali a ƙasarsa.
Yayin da suke kira ga Tchiani ya ba da haƙuri nan take, dattawan Arewacin Najeriya sun bayyana irin waɗannan maganganu da cewa za su iya jawo fitintinu.
Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa hadin guiwa tsakakin Hon. Yusuf Abubakar da ya hada taron, Alhaji Yasir Ramadan Kano (kungiyar matasa), da Injiniya Mustafa Aliyu Dutsin-Ma (Kungiyar Ci Gaban Dattawan Arewa), wadda aka karanta wa manema labarai a ƙarshen taro na 8 na haɗin guiwar Kungiyar Matasa ta Arewa don Zaman Lafiya da Ci Gaban Siyasa, da kuma Kungiyar Ci Gaban Dattawan Arewa da aka gudanar a Kaduna.
A cewar kungiyoyin, zargin da Tchiani ya yi ba su da tushe kuma suna iya tayar da tarzoma a Najeriya.
“Mu dai matsayinmu a wannan batu shi ne cikakken goyon baya da amincewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman da irin manyan ayyukan ci gaba da yake yi, tabbatar da haɗin kan siyasa, tsaro, da dawo da zaman lafiya a yankinmu mai fama da rikici, wato Arewa.”
“Mun yi kira ga Shugaban Jamhuriyar Nijar da ya ba Najeriya haƙuri kuma ya daina ƙirƙirar matsalolin rashin jituwa tsakanin waɗannan ƙasashen biyu ‘yan uwa da ke da tarihin haɗin kai da fahimtar juna tun shekaru da dama da suka gabata. Muna so mu gargadi wasu ƙungiyoyi da ke ɓoye ƙarƙashin wasu mummunar niyya da su daina hura wutar kiyayya, ganin illarta ga haɗin kai da rayuwarmu a matsayin mutane da ƙasa baki ɗaya.
Kungiyoyin sun kuma jinjinawa mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu bisa jajircewarsa wajen dawo da tsaro Arewa.
Dattijan Arewa, Matasa sun nemi shugaban Nijar ta nemi afuwar Najeriya


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading