Direban gidan gwamnatin Taraba ya fadi ya mutu yayin da ya samu labarin mutuwar kanwar gwamnan

Wani ifti’in ya sake afkawa iyalan gwamnan jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, yayin da rahotanni suka ce direban mahaifiyar gwamnan ya fadi ya mutu bayan samun labarin rasuwar ‘yar uwar gwamnan, Atsi Kefas, wadda ta samu rauni sanadiyar harbin kan mai uwa da wabi da yan sanda sukayi.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a gidan T.Y. Danjuma da ke Abuja.
Majiya mai tushe a wurin ta ce direban mai suna Abraham ya fadi ne bayan da ya yi ihu a lokacin daya samu Labarin matuwar.
Abraham, dan asalin garin Wukari, shine yake tuka motar da marigayiyar take cikin a lokacin da harsashi ya afkawa mata a hanyar Wukari zuwa Kente a ranar 5 ga Disamba, 2024.
Abraham yana aiki a matsayin direba a ayarin matar gwamnan tun lokacin da Gwamna Kefas ya karbi mulki a shekarar 2023.
Direban gidan gwamnatin Taraba ya fadi ya mutu yayin da ya samu labarin mutuwar kanwar gwamnan


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading