Cibiyar kare hakkin Dan Adam da wayar da kan yan kasa wato CHRICED ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta gaggauta aiwatar da gyare-gyare a cikin tsarin shari’ar Najeriya, domin tabbatar da adalci da kuma karko a tsarin dimokuradiyya.
Cibiyar ta fadi hakan ne a cikin jawabin da Comrade Ibrahim M. Zikirullahi, Daraktan Gidauniyar CHRICED ya gabatar a ranar Talata, 31 ga Disamba, 2024, a Abuja.
Ya yayin bayanin sa yayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta aiwatar da muhimman gyare-gyare a cikin tsarin shari’a, domin tabbatar da adalci da inganta dimokuradiyya a kasar.
Ya bayyana cewa tsarin shari’ar Najeriya yana fuskantar matsaloli na rashin gaskiya da cin hanci, wanda ke hana mutane samun adalci a gaban kotuna.
Zikirullahi ya ce, “dole ne a mayar da hankali kan gyara tsarin shari’a domin tabbatar da cewa kowanne dan kasa yana da damar samun adalci ba tare da wani shakku ko jinkiri ba.”
A cikin jawabin, Zikirullahi ya yi nuni da yadda tsarin shari’a ke fama da matsalolin rashin kwararrun ma’aikatan shari’a da cin hanci a cikin wasu bangarorin. “Wannan ya jawo cewa, mutane da dama suna jin tsoron cewa kotunan kasar ba za su iya bayar da adalci ba, saboda gurbatar da ke cikin tsarin,” in ji shi.
Cibiyar ta yi nuni da yadda za a iya magance wannan matsala ta hanyar aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar shari’a da tabbatar da cewa dukkanin al’amuran shari’a suna gudana bisa gaskiya da tsari mai kyau.
Zikirullahi ya ce, “bari mu fara da tabbatar da zaman lafiya a cikin kotuna, da kuma inganta yadda ake gudanar da shari’o’in cikin gaggawa don rage lokacin da ake dauka wajen yanke hukunci.”
Cibiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan tabbatar da cewa dukkanin jami’an shari’a suna aiki cikin gaskiya, tare da daukar matakai na hukunta duk wanda aka samu da laifin cin hanci ko yi wa shari’a barna.
“A gaskiya, idan gwamnati tana son ci gaban dimokuradiyya, dole ne ta dauki mataki mai tsauri akan masu gurbata tsarin shari’a,” Zikirullahi ya bayyana.
A karshe, Zikirullahi ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya mai da hankali kan wannan matsala a shekarar 2025.
“Daga cikin abubuwan da za su sanya Najeriya ta ci gaba da zama kasa mai ingantacciyar dimokuradiyya, yana da muhimmanci mu tabbatar da cewa tsarin shari’a yana aiki cikin gaskiya da rikon amana,” in ji shi.
Dole ne a gyara hukumomin shari’a don tabbatar da adalci a Najeriya – CHRICED
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.