Gamayyar kungiyoyin farar hular ta jihar Kano, ta bukaci gwamnati ta hanzarta kafa hukumar masu bukata ta musamman a jihar,
Shugaban gamayyar, Comrade Muhammad Bello ya bukaci haka a wani taron manema labarai yau a cibiyar ‘yan jaridu da ke nan Kano.
Comrade Salisu Yusuf, shi ne babban sakataren gamayyar, ya kuma yi wa Premier Radio karin bayani kan wannan bukata.
Comrade Salisu, ya kara da cewa, tasirin jinkirta kafa hukumar na haddasa koma-baya ga masu bukata ta musamman, da ma jihar Kano bakidaya.
Taron ya samu halatar masu ruwa-da-tsaki a bangarorin masu bukata ta musamman, da ‘yan jarida da dama a nan Kano.
Gamayyar fararen hula sun nemi gwamna Abba ya kafa hukumar masu bukata ta musamman
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.