Gobara ta babbake sashen kasuwar ‘yan katako a Legas

Gobara ta lakume kasuwar katako da ke kan hanyar Pipeline Street a yankin Ikotun na Jihar Legas a ranar Alhamis, inda ta lalata wani ɓangare na kasuwar.
A cewar wata sanarwa da Babban sakatare na hukumar ba da aagajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya fitar, gobarar ta shafi shaguna huɗu kacal.
Ya ce, saurin amsa kiran agajin hukumar daga Igando, tare da haɗin kai da sauran ma’aikatan da suka isa wurin, sun hana wutar bazuwa zuwa gine-ginen da ke makwabtaka da wurin.
Babban Sakatare na LASEMA ya lura cewa binciken farko bai gano musabbabin gobarar ba har zuwa lokacin da aka bayar da wannan rahoto.
Ya kuma bayyana cewa babu asarar rayuka ko rauni da aka samu sakamakon wannan gobarar.
Wannan yana zuwa ne bayan wani rahoto na tashin gobara a ofishin hukumar bincike kan nasana’antu ta kasa (FIIRO) da ke Oshodi a safiyar ranar.
LASEMA ta tabbatar da cewa gobarar ta tashi sakamakon yawan amfani da janareta da ya yi zafi.
Ita ma wannan gobarar an shawo kanta, babu asarar rayuka ko raunuka da aka samu sakamakon lamarin.
Gobara ta babbake sashen kasuwar ‘yan katako a Legas


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading