Kar ku fada tarkon makiya Kano – Sarki Sanusi ga Mabiyansa

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi ga magoya bayansa da kada su dauki doka a hannunsu bayan sojoji sun mamaye gidansa.
Muhammadu Sanusi II ya yi zargin akwai wasu mutane masu burin ganin jihar Kano a cikin tashin hankali.
“Na yi gargadin ku da kada ku fada cikin tarkon abokan gaba na Kano, wadanda suke son ganin Kano ta kone,” in ji Sarkin.
Ya ce mutanen suna kaunar su ka ana lashe rayukan yan ba ruwana da lalata dukiyar mutanen jihar,” in ji Sarkin Kano yayin gabatar da khutbar Juma’a a Masallacin Jumma’a na masarauta.
Sarkin Kano ya ce an san musulmi da juriya da son zaman lafiya a kowane irin yanayi.
“Shi ya sa, duk wanda yake sonmu kuma yake goyon bayanmu, muna rokon sa da ya guji tashin hankali a kowane lokaci, ko da menene,” in ji Sarki Muhammadu Sanusi II.
Kar ku fada tarkon makiya Kano – Sarki Sanusi ga Mabiyansa


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading