Wani kuduri da ke neman gyara dokar Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Kasa (UBEC) ya samu amincewa da karatonsa na biyu a Majalisar Dattijai.
Kudurin ya samu gabatarwa daga Sanata Adamu Lawal Usman, wanda ke wakiltar yankin Kaduna Tsakiya a Majalisar Dattijai.
An gabatar da gyare-gyaren da suka shafi sassa na 2, 3, 7, 9, 11, da 16 na dokar, wanda suke da nufin inganta ilimin yara kanana, tsare yadda ake naɗa mambobin hukumar, da tabbatar da bin ka’idojin da hukumomin aiwatarwa ke amfani dasu.
Haka kuma, kudirin dokar na bada shawarar karin kudade daga kashi biyu zuwa kashi biyar, tare da tura kudaden tallafi kai tsaye zuwa bangaren ilimi na kananan hukumomi.
Bayan wucewa karatu na biyu, an tura kudirin dokar zuwa kwamitin majalisar dattawa kan Ilimin Sakandare da Na Asali don ci gaba da aikin doka
Kuɗirin gyaran UBEC ya wuce karatu na biyu a majalisa
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.