Kwamishinar mata a Bayelsa ta rasu

Kwamishinar mata ta jihar Bayelsa, Elizabeth Bidei, ta rasu.

An sanar da rasuwarta ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Labarai, Ebiuwou Koku-Obiyai, ya fitar a ranar Talata.

Obiyai ya bayyana alhini tare da mika ta’aziyya ga iyalinta, musamman mijinta, Jackson Bidei, da yaran su.

Sai dai ba a bayyana dalilin rasuwarta ko ranar da ta rasu ba.

Sanarwar ta ce: “Zuciyoyinmu na tare da iyalin marigayiyar. Muna addu’a a gare su a wannan lokaci na alhini.

“Yayin da muke yi mata rakiya, za mu yi kewarta a matsayinta na mai kishin kasa, yar siyasa, Da ta yi aiki tuƙuru wajen inganta walwalar mata da karfafa mata a jihar mu.”
Kwamishinar mata a Bayelsa ta rasu


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading