Muna dab da rasa zangon karatu saboda kasa biyan kudin makaranta – Daliban BUK

Daliban da suke karatu a jami’ar Bayero da ke jihar kano sun koka kan yadda suke dab da asarar shekara guda ko kuma kora daga jami’ar sakamakon rashin biyan kudin makaranta na wannan shekarar.
Shugaban majalisar daliban yan asalin jihar kano reshen jami’ar Bayero ta kano kwamared Mahumud sunusi gama ne ya bayyana haka.
Mahmud Gama ya bayyana ce wa bayan d’aga musu kafa da makarantar tayi na tsawon zangon karatu guda yanzu sati uku kawai ya rage musu gashi kuma gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na biya musu kudin.
Gama ya bukaci masu hannu da shuni da masu madafun iko dasu taimakawa daliban don kada su rasa damar da suke da ita.
Idan za’a iya tunawa Gwamnatin kano ta biyawa daliban jami’ar sama da dubu bakwai kudin makarantar sakamakon gaza biyan kudin da sukayi a shekarar 2023 saidai a wannan karon daliban basu samu wannan taimakon ba.
Muna dab da rasa zangon karatu saboda kasa biyan kudin makaranta – Daliban BUK


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading