Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta umarci dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya, na gwamnati da masu zaman kansu, da su fara gwajin COVID-19 akan duk wadanda ake zargi yana dauke da cutar.
A wata sanarwa da aka fitar da yammacin ranar Asabar, mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar, Dr Jide Idris, hukumar ta ce ya kamata a aika duk wani samfurin da ya dace zuwa dakin gwaje-gwaje na NCDC da sauran dakunan gwaje-gwajen kiwon lafiyar jama’a da aka amince da su domin tantancewa.
Ya ce har yanzu ba a gano nau’in cutar Covid-19 da ake kira SARS-CoV-2 XEC sub-variant a Najeriya ba.
Ya ce sanarwar ta zama dole don kawar da fargabar da aka haifar a kafofin sada zumunta game da bambance-bambancen Covid-19 da aka ruwaito yana yaduwa a Australia.
Shugaban na NCDC ya ce kungiyar ta COVID-19 Technical Working Group (COVID-19 TWG) za ta ci gaba da sanya ido tare da gudanar da nazarin bayanan a duk fadin duniya da kuma fadin kasar don tabbatar da lafiyar al’umma .
NCDC ta bukaci a zarfafa bincike kan wadanda ake zargi suna dauke da COVID-19
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.