Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kakkausar suka kan matakin Gwamnatin Tarayya na rashin ware wani kaso ga yankin Arewa ta tsakiya a kasafin kudin 2025
A wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X, Obi ya bayyana wannan mataki a matsayin nuna wariya da cutarwa ga cigaba da zaman lafiyar da ake bukata don cigaban Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ja hankali kan manyan kalubalen da yankin Arewa ta tsakiya ke fuskanta, musamman hare-haren ta’addanci, ‘yan fashi, da rikicin kabilanci, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da kuma raba dubban iyalai da gidajensu.
Jihohi irin su Filato, Benuwai, Kogi, da Neja sun fi shan wahala, inda dubban jama’a ke zama a sansanonin ‘yan gudun hijira.
“Rashin sanya Hukumar cigaban Yankin Arewa ta tsakiya a cikin kasafin kudin 2025 abun damuwa, ne kuma dole ne a gyara nan take,” inji Peter Obi.
A cewar Obi, Gwamnatin Tarayya ta ware jimillar Naira tiriliyan ₦2.493 ga hukumomin cigaban yankuna guda biyar a kasafin kudin 2025, amma ta bar Arewa ta tsakiya a baya.
Wannan, a cewarsa, ya yi watsi da bukatun yankin da ke da matukar muhimmanci ga cigaban Najeriya baki daya.
“Wannan yankin da ke matsayin ginshikin noma a Najeriya ya cancanci samun goyon baya mai karfi don tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da cigaba, wanda zai amfani kasa baki daya,” ya kara da cewa.
Obi ya bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su duba wannan lamari cikin gaggawa don gyara kuskuren da ka iya haifar da illa ga yankin da kasa baki daya.
Obi ya zargi gwamnatin tarayya da watsi da yankin Arewa ta tsakiya
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.