Shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kudi ranar Talata

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2025 a gaban Majalisun Dokoki ƙasar ranar Talata mai zuwa.
Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisa a ranar Alhamis.
Akpabio ya ce, a farko, za su taru a dakin majalisar dattijai, daga nan kuma su zarce zuwa dakin majalisar wakilai don gudanar da zaman hadin gwiwar.
“Shugaban kasa ya sanar da aniyarsa ga Majalisar Dokoki ta Kasa na gabatar da kasafin kudin 2025 a zaman hadin gwiwa a ranar 17 ga Disamba, 2024,” in ji shi.
A baya, Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ya ce kasafin kuɗin ya kai Naira tiriliyan 47.9.
Shugaba Tinubu zai gabatar da kasafin kudi ranar Talata


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading