Wike zai raba motoci ga hukumomin tsaro a Abuja

Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Ezenwo Wike, zai raba sabbin motocin aiki guda 50 ga hukumomin tsaro daban-daban a Abuja.
Wannan bayanin ya fito ne daga mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka a ranar Alhamis.
Olayinka ya wallafa hotunan sabbin motocin da aka shirya don rabawa.
Ya ce motocin za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata a FCT.
“Ko a yanzu haka, Ministan FCT, Nyesom Wike, zai raba waɗannan sabbin motocin guda 50 ga hukumomin tsaro domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu,” in ji Olayinka.
Wike zai raba motoci ga hukumomin tsaro a Abuja


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading