Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Anambra

‘Yan bindiga sun kashe mutane bakwai, ciki har da fararen hula biyu da jami’an tsaro biyar a karamar hukumar Ihiala, ta jihar Anambra.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Litinin yayin da fararen hular ke cikin wani gida suna shirin wata jana’iza da aka tsara gudanarwa a ranar 2 ga watan Janairu, 2025.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna gawar wasu mambobin kungiyar tsaro ta jihar Anambra (AVG), wadanda su ma suka rasa rayukansu a harin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Nnaghe Obono Itam, ya bayar da umarnin a fara farautar wadanda suka aikata harin.
“da musalin karfe 11:20 na safe, ‘yan bindigar sun far wa wajen da ake shirin jana’iza, inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa. Sun kuma harbi wasu jami’an tsaro guda biyu,” in ji SP Ikenga.
Kakakin ya kara da cewa tawagar tsaro ta hadin gwiwa ta ceto wani mutum da aka harba, wanda yanzu haka yana karbar magani a asibiti.
Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Anambra


Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe to get the latest posts sent to your email.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Discover more from viewnowafrica.com.ng

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading