Hukumar ‘Yan sandan Jihar Edo ta damke wani mutum mai suna Theophilus Osazuwa bisa zargin kashe ɗansa mai shekaru huɗu.
Kamar yadda kakakin rundunar, Moses Yamu, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, an ce Osazuwa ya aikata wannan laifi ne a yayin da yake ƙarƙashin tasirin miyagun kwayoyi.
Yamu ya ce lamarin ya faru ne a kimanin karfe 12:30 na rana a ranar Talata, lokacin da Osazuwa ya dawo gidansa dake Ogbeson Quarters, a gefen Titin Benin-Agbor, a Birnin Benin, sannan ya faɗi cikin wani yanayi na tashin hankali.
A cikin wannan yanayi, an ce wanda ake zargi ya yi ƙarar “Holy Ghost fire,” sannan ya kama ɗansa, Testimony Osazuwa, ya jefa shi a bango, wanda ya haifar da mutuwar yaron.
Kakakin rundunar ya ce, “Rundunar ‘Yan sandan Edo ta cafke Theophilus Osazuwa na Ogbeson Quarters, a gefen Titin Benin-Agbor, Birnin Benin, bisa zargin kashe ɗansa mai suna Testimony Osazuwa.
“An ce wanda ake zargin ya isa gida a ranar 24 ga Disamba, 2024, karfe 12:30 na rana, sannan ya shiga cikin magagi yana ƙiran ‘Holy Ghost fire,’ sannan ya kama ɗansa mai shekara huɗu ya jefa shi a bango. An kai yaron asibiti, amma an tabbatar da mutuwarsa kafin mu iso.
“Binciken farko ya nuna cewa wannan matashin wanda aka sani da amfani da kwayoyi irin su ‘ice’ da sauran miyagun kwayoyi yana yiwuwa ya aikata wannan laifi ne ƙarƙashin tasirin waɗannan kwayoyi.”
Kakakin ya ƙara da cewa, kwamishinan ‘Yan sanda na jihar, Umoru Ozigi, yayi gargadi ga matasa game da haɗarin amfani da miyagun kwayoyi, yana mai jaddada mummunan tasirinsu ga lafiya da kuma haɗarin da suke kawo wa rayuwarsu da kuma al’umma.
’Yan sanda sun damke wani da zargin kashe ɗansa a Edo
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.