Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ce gwamnatinsa za ta mai da hankali kan manufofi da shirye-shirye da za su kawo ci gaban da zai amfanar da kowa da kowa, tare da bunkasa damar tattalin arzikin al’ummar jihar.
A cikin sakon sabuwar shekara ga mutanen jihar, Gwamna Nwifuru ya danganta nasarorin da gwamnatinsa ta samu har zuwa yanzu ga goyon baya da addu’o’in al’umma.
“Yayinda muke shiga sabuwar shekara ta 2025, ina tura gaisuwar zagayowar shekara ga kowanne dan kasa da mazaunin jihar mu mai girma.
“Wannan lokaci ne na tunani da sabuntawa, dama ce ta tsara sabuwar hanya don ci gaban kai da na kowa da kowa bisa tsarin bukatun al’umma.
“A cikin shekarar 2024, ta hanyar goyon bayan ku, addu’o’in ku da karfafa gwiwar ku, mun sami sabbin nasarori, kuma mun dauki matakin gagarumin ci gaba a dukkan fannonin shugabanci.”
Yayin da yake jaddada wasu daga cikin ayyukan gwamnatin sa na shekarar da ta gabata, Gwamna Nwifuru ya bayyana cewa sama da mutane 25,000 daga cikin al’ummar jihar an saka su cikin wani tsarin tattalin arziki mai dorewa don inganta ci gaba da arziki.
“Na ayyana wannan sabuwar shekara a matsayin shekara wadda za a samu ci gaban da bai taba faruwa ba, da bunkasar al’umma da kuma sauyi mai girma a dukkanin sassan jihar,” in ji Gwamna Nwifuru.
Zan maida hankali kan manufofi da shirye-shirye masu inganta ci gaba a 2025 – Gwamnan Ebonyi
Discover more from viewnowafrica.com.ng
Subscribe to get the latest posts sent to your email.